


COVID19: HARAMUN NE WANI DAGA KANO YA FITA DAGA CIKINTA A YANZU – Dr Ahmad Gumi
Saboda yanzu jama’ar Kano sun tabbatar da gaskiyar Corona ya sanya wadansu daga birni suna guduwa kauyuka, wasu na tsallakawa wasu jihohi, ga sakon Manzon Allah SAW gare ku da sauran jama’a da suke cikin garin da ake yin annoba.
DAY 09 – DA DAN BIDI’A DA MASU RABUWAR KAI DUK MAKOMARSU WUTA – RAMADAN TAFSIR 2020 (29-04-2020)
Wannan shine tafsirin Alkur’ani mai girma da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya gabatar yau Larabar 29-04-2020 inda yayi fassara a cikin Suratut Taubah kuma ya jawo hankali game da matsalar rabuwar kai, bidi’a da shi’a da makamantansu
GA AIKIN LADA DA YA FI HAJJI DA UMRAH KOWA ZAI IYA – Dr. Ahmad Gumi
A cikin ayyukan ibada da jama’a suke kokarin yi da kuma fatan kankare zunubi babu kamar aikin Hajji ko Umrah shi yasa mutane da dama kowace shekara suke da burin zuwa Makka don yin wannan ibada, amma kuma akwai ibadar da ta fisu a wurin Allah don tanayi abinda Hajji da Umrah suke yi kuma […]
DA ME ZAKA NEMI KUSANCI GA ALLAH? – Dr. Ahmad Gumi
In dai Allah ake numa da kusanci da kuma neman ya yarda da bawansa da kuma karbar Addu’arsa, to zai nemi kusancin Allah da wadannan ayyukan kuma da sune Allah zai karbe shi ya kuma amsa masa dukkan bukatunsa, wannan sharadin tabbatacce ne daga Manzon Allah SAW
TSADAR KAYAN ABINCI: KAYYADE FARASHI WAJIBI NE YANZU – Dr. Ahmad Gumi
Lokacin da Malam yake bayani game da Hadisin Manzon Allah da ya ce ba zai kayyade farashin kaya ga mutanen Madina ba, a gefe guda Imamu Malik ya fadi dalilin Manzon Allah SAW na fadan haka, da kuma dalilin da zai sanya a kayyade farashi a wurin ‘yan kasuwa.
DAY 08 – SADAKA NA TSARKAKE MUTANE DA SAMUN LADA – RAMADAN TAFSIR 1441-2020 (28/04/2020)
Wannan shine Tafsirin Alkur’ani mai girma da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya gabatar yau Talata 28/04/2020 a cikin Suratut Taubah aya ta 102-105
MATSALAR RASHIN ZAMA GABAN MALAMAI – Dr. Ahmad Gumi
A cikin wannan video zamu ji yadda Sahabban Manzon Allah suka samu tarbiya a gare shi, da kuma dalilin da yasa Larabawan daji suka fi kafirci da munafinci da kamanceceniya da ke tsakanin wanda ya yi karatu a gaban malami da wanda ya koyi karatu a gaban na’ura ko dakin litattafai.
HUKUNCIN WANKIN CIKI KO BARI GA MACE ME AZUMI – Dr. Ahmad Gumi
Tambayar da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya amsa yau game da macen da tayi barin ciki kuma wani abu ya yare a cikinta malaman kiyon lafiya suka ce se anyi mata wankin ciki gashi kuma watan azumi ake, kuma tana ganin jini har yanzu?
A SHIGO DA ABINCI MUTANE NA CIKIN WAHALA – Dr. Ahmad Gumi
Wannan kira ne da Malam yayi akan wannan gwamnatin da ta taimaka ta wadata Al’umma da abinci kasancewar wannan annoba ta sanya kayan abinci a cikin gida yayi tsada. Malam yayi kira da ta taimaka ta shigo da abinci don ya karye ya wadata ga al’umma.